Gyara Bangaren Shari'a Zai Kawo Gyaran Cin Hanci Da Tsaro.

Ba Wannan ne Lokaci na farko ba da Shugabanni suke daukan alkawari Wajen kawo Karshen Cin Hanci da Sha’anin Tsaro, Kowane Shugaba yanabin wasu matakai domin ganin ya cimma nasarar hakan, amma wasu kuma kan samu nakasu Wajen Hanyoyin Cimma Nasarar, imma de daga 6angarensu ko kuma daga Hukumomin da nauyin hakan ke rataya akansu, Wannan ta sanya madadin abubuwan sudinga raguwa kusan sede ace Kullum kara karuwa sukeyi, Matsalar tsaro tuni ta sanya Kasar cikin tsaka me wuya,
musamman awasu Sassan arewacin Kasar nan, hakan ta sanya Kullum rayukan Al’umma na Salwanta, koda banda balahirar Boko Haram
akwae fadace-fadace masu nasaba da Kabilanci agaruruwa irinsu Jos, Nassarawa da Benue, dawasu sassan yankin Kaduna, Wannan ta Sanya abun yazama yayi kaka-gida a6angaren, idan na kintata dede tun Lokacin Obasanjo har yanzu bamu sami Karfin Tsaron damuke bukataba,
takowace fuska matsaloli dasuka shafi Siyasa da Kabilanci na taka mahimmiyar rawa wajen kara hura wutar rikicin, Matsalar Kabilanci Akasar nan Kusan tana bada goyon baya wajen kasa kawo karshen fitintinun, yayinda kowa ke kokarin kare nasa koda ace nasan ne da lefi, wannan shine babban kuskuren da Shugabannin Kabilu da Shugabannin Addinai Suke tafkawa, aYayinda sukuma daya 6angaren Kullum babban burinsu asamu wanda basaso da laifi kodon su dinga yayata hakan amatsayin kare nasu 6angaren.
     Haka idan kadubi matsalar Cin Hanci da Rashawa Kullum kara tashi yakeyi, anutse idan kayi tunani shima zakaga Kabilanci yataka mahimmiyar rawa wajen kara ha6akashi, duk Cancantar mutum idan gaban wanda banasaba, misali ba Kabilarsaba ko Addininsaba to anan zakaga zallar Wariyar launin fata, karshe yahana wanda ba nasan ba wannan dama, yakawo nasa koda bai Cancanci wannan gurinba, inde ze bashi na gwamna masu gidan rana(kudi).. Misali amatsayina na Mailafiya dana taho daga 6angaren Arewa, inason Ci-gaban yankin
amatsayinsa na Yankina, amma kuma Kullum
abin Kallona shine menene makomar Kasata? Babu kasar dazataci gaba batare data hade kantaba , haka babu wata al’umma dazata cimma kyawawan muradunta batare data Samu Ci- gaban Kasa ta fuskar kawar da 6angaranci da Kabilanci ba, Sannan babu Al’ummar Ko Kasar dazata Samar da Kyawun Shugabanci wa al’ummarta batare data Girmama 6angaren SHARI’A ba, tsayar da DOKA da ODA inji Hausawa shine karshen duk wani hargitsi da tashin- tashina, duk wanda yataka dokar Kasa duk Mulkinsa da Girmansa to Doka tahau Kansa koda hakan na nufin karshen Mulkinsa ko Martabarsa, kodaga wane Kabila ko Yanki yafito Doka itace zata hukuntashi dede da Karantsayen dayayi mata, Wannan shine kadai zai Kawo tarnaqin da ake ciki wajen Kawo gyara Asha’anin Tsaro da Cin Hanci da kar6ar Rashawa.
   Lalle Yakamata dame girma Shugaba Buhari Ya Gyara harkokin 6angaren Shari’a na Kasar nan, tareda basu duk irin karfin dasuke bukata, dukda Kasancewar itama 6angaren shari’ar cike take da Kalubale da magudin shari’o’I, hakika naji dadin dauko mutane irinsu Abubakar Malami SAN da Femi Falana SAN da Shugaba Buhari yayi, hakika mutane ne dasuka dade cikin Harkokin Shari’ar Kasar nan, sunada wayewa tareda Sanin makamar Hanyoyin daza’abi don Kawo gyara da Sauyi Wajen harkokin Shari’a a Kasar nan, Femi Falana Esq anyi masa SAN a 2012, Abubakar Malami kuwa a 2008, hakika Wannan gogewar kadai ta Isa sukai 6angaren Shari’a Tudun Mun Tsira.

By

Sunusi Mailafiya

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*