Dan Sanda Ya Bindige Matarsa Har Lahira

Wani dan sanda mai suna Abdul’ziz ya harbe tsohuwar matarsa har lahira a barikin ‘yan sanda da ke Kaduna. Wannan ta’asa ta faru ne a yayin da marigayiyar mai suna Safiya ta zo barikin don kwasar kayanta, inda ta zo tare da abokan rakiya kimanin mutane biyar do taya ta kwasar kayan. Kafin ta kai ga shiga gidan, kai tsaye ta tafi wajen babban ofisa mai kula da harkokin gidaje na barikin don shaida masa abinda ke tafe da ita. Nan take ofisa ya kira tsohon maigidan nata, ya kuma hada su da wasu ‘yan sanda biyu don yi musu rakiya kai tsaye zuwa cikin gidan don gudun ka da wani abu maras dadi ya faru a tsakaninsu. ‘Yan sandan da suka raka su, daya na dauke da bindiga, dayan kuma babu bindiga a tare da shi.
A daidai lokacin da suka fara kwasar kayan, shi ma tsohon maigidan nata ya sa hannu yana taya su kwasar kayan ana ta fita da su kamar abin arziki, ashe fakonta ya ke yi ba tare da kowa ya sani ba. kamar yadda daya daga cikin wadanda marigayiyar ta tafi da su don su taimaka mata wajen kwasar kayan ya bayyana, ‘Ina kokarin cire gado ne Abdul’aziz ya ce da ni yana da wata ajiya a karkashin gadon, na jira ya dauka tukuna. Ashe bindiga zai dauko, ba tare da wani bata lokaci ba nan take ya harbe tsohuwar matar tasa Safiya har lahira daidai lokacin da take tattara wasu karikicenta a dakin girki, ya kuma ruga waje da gudu yana ihu yana cewa, ‘Wayyo Allah na, jama’a ku taimake ni na kashe maman Zainab ni ma ku taimaka ku kashe ni.’ Daga nan ya sake komawa cikin gidan yana ihu, ya sake harba wani harshashin sama ya kuma sake fitowa waje a ajiye bindigar ya kama katangar barikin nasu na ‘yan sanda ya tsere, inda daga bisani kuma ya kai kansa zuwz shalkwatar ‘yan sandan ciki. In ji kafintan da ya raka ta.’

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*