Dalilin Da Yasa Ali Nuhu Yaza Ma Tauraro A Najeriya

Abu na farko da yasa Ali Nuhu yayi tasiri a Kasar hausa da Najeriya baki daya shine Ilimi, saboda a duniya ba abunda yake tasiri sai da ilimi kuma Ali Nuhu ya kasance tun lokacin da ya fara fim mutun ne mai ilimi sanan kuma yana anfani da ilimin nasa.
Ali Nuhu na bin zamani, duk a Jaruman Kasar Hausa babu kamar Ali Nuhu wajen bin zamani saboda duk wasu kafofin sada zumunta zaka samu shine gaba. Kamar misali shi kadai ne yake da shafin na yanar gizo www.alinuhu.net sannan shi kadai ne jarumin da Kamfanin Twitter suka tantance. Wannan ya nuna irin gwazo da yake nunawa wajen sada zumunta. Idan kana bin Ali Nuhu a Twitter zaka san da hakan saboda kusan koda yaushe yana ganawa da masoyanshi. Hakan duk a Facebook, Twitter, Instagram.
Saukin kan Ali Nuhu da rashin girman kai a matsayin sa na Jarumi nada cikin abunda yasa Allah yake kara dora sa akan wasu taurari. Duk wanda yasan Ali Nuhu zai fada maka cewa bashi da girman kai.
Ina ganin wannan kadan daga cikin abubuwan da zan fada game da Ali Nuhu amma a takai ce Jarumi ne mai tafiya da zamani.
naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*