An Rufe Makarantu Karantu 150 A Diffa

An rufe makarantu 150 a yankin Diffa na jamhuriyar Nijar saboda hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram.
Ofishin da ke kula harkokin jin kai na majalisar dinkin duniya wanda ya bayyana haka a cikin wata sanarwa, ya ce rufe makarantun ya janyo yara 12,631 ba sa zuwa makaranta.
Hukumar ta ce lamarin kuma ya janyo malamai sun kaurace wa makarantun a yayin da mutane kuma ke ci gaba da ficewa daga yankin.
Sanarwar ta ce “Daliban a yanzu suna sansanonin ‘yan gudun hijira kuma babu makarantu a can.”
An rufe makarantu da dama a Najeriya da Nijar sakamakon hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram abin da ya jefa makomar dubban yara cikin rashin tabbas.
A yanzu haka dai gwamnatin Nijar na aiki tare da majalisar dinkin duniya domin fitar da wani tsari ta yadda yaran za su koma yin karantu a wasu yankunan da babu hadari.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*