An kafa dokar ta baci ta kwanaki 10 a Mali

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya sanar da kafa dokar ta-baci ta tsawon kwanaki 10, tare da zaman makoki na kwanaki uku bayan garkuwa da mutane da wasu ‘yan bindiga suka yi a wani otel da ke birnin Bamako, lamarin da a hukumance aka ce ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 21 yayin da wasu majiyoyi ke cewa sun kai 27.
Majiyoyin tsaro sun ce daga cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai Ba’amurke daya, da dan kasar Belgium daya da kuma wasu China uku.
Jami’an tsaron kasar Mali da kuma na kasashen ketare, sun share tsawon yinin juma’a kafin ceto mutane 170 da aka yi garkuwa da su a Hotel Radisson da ke birnin na Bamako.
Mutanen da ke cikin wannan otel lokacin faruwar lamarin, sun fito ne daga kasashen duniya 14.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*