An gurfanar da wani mutum da yayi fice wajen yankan gaban mata a Afrika ta Kudu

An gurfanar da wani mutum a gaban Kotu a kasar Afrika ta Kudu a yau Laraba bisa samun shi da akayi da sassan farjin mata har guda 21 a gidansa,
Mutumin mai kimanin shekaru 63 dan asalin kasar Denmark, ya shiga hannu ne a watan Satumba bayan da aka kama shi da sassan mata da kwayoyi masu sa barci da kuma kayan yin fida,
An ruwaito cewa matar, mutumin mai suna Anna Matseliso Molise yar kimanin shekaru 28 ce ta sanar da yan sanda cewa mai gidan nata ya danne ta ya yanke mata farji,
Bayanai sunce bayan da jami’an yan sanda suka kai sumame a gidan Mista Peter Frederiksensai, sai sukayi kicibis da wadannan abubuwa, wanda hakan tasa suka gurfanar da shi, sai dai kuma daga bisani wasu yan bindiga sun harbe matar mutumin har lahira lokacinda zata je gabatar da shaida akan mai gidan nata a gaban Kotun,
Mai magana da yawun rundunar yan sanda a kasar, Misis Masilea Langa ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta kara da cewa a binciken da suka gudanar sun gano mutumin nada shagon saida bindigogi,
Tace galibin matan da Frederiksen yayi wa wannan aika-aika yan yankin birnin Lesotho ne kuma sau tari sai yana tsakiyar lalata da su idan hankalinsu ya gushe sai ya aiwatar da wannan danyen aikin,
Ta kara da cewa basu san ko yan matan da mutumin ya yiwa wannan danyen aikin sun rayu ba,
Sai dai tace mutumin ya adana bayanai akan duk Matan da ya yiwa wannan aika-aika tun daga matar da ya soma yanke mawa a shekarar 2010.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*