Zan iya yin kuka idan aka tafi hutu -Wenger

Manajan Arsenal, Arsene Wenger, ya ce zai iya yin kuka
idan har hukumar shirya gasar Premier ta kirkiro da
hutun karshen shekara.
Kulob din sa dai na da wasanni 7 tsakanin ranakun 13 ga
watan Disamba da 16 ga watan Janairu, ciki har da
wasanni uku cikin kwanaki bakwai a watan Disamba.
”Buga wasanni a lokacin bukukuwan kirsimeti da sabuwar
shekara al’ada ce ta kasar Ingila da kuma ta kwallon kafa,
kuma ni ina son in ci gaba da bin ta” In ji Wenger.
Amma manajan kulob din Manchester United, Louis van
Gaal ya ce rashin bayar da hutun wasanni a karshen
shekara a Ingila a zaman wata mummunar al’ada.
Su ma Manchester United suna da wasanni bakwai
tsakanin ranakkun 13 ga watan Disamba da kuma 16 ga
watan Junairun shekarar 2016, inda suke da wasannin
uku jere a cikin kwanaki tara tsakanin ranakun 19 da 28
ga watan Disamba.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*