Yanda Mutane 16 Suka Mutu A Harin Kunar Bakin Wake A Adamawa

Mutum goma sha shida ne rahotanni suka bayyana cewa sun mutu a wani harin kunar bakin waken da wasu ‘yan mata biyu suka kai a kauyen Dar da ke Karamar Hukumar Madagali ta jihar Adamawa. Wani ganau ya ce an kai harin ne da misalin goma na dare, wanda yayi sanadin mutuwar masu kai harin da wasu mutanen 14 nan take.
Da yake yi wa manema labarai karin bayani, Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Madagali, Hon. Maina Ularamu ya bayyana cewa mutum 12 ne suka mutu a harin. Ya ce, sakamakon tashin bom din, jama’a sun tarwatse, inda wasu suka gudu cikin daji, baya ga wadanda suke neman dauki bayan jikkata da munanan raunukan da suka samu a harin.
Majiyar ta LEADERSHIP Hausa ta bayyana cewa a ranar Juma’a ma ‘yan bindigar sun kai wani harin a garin Komda da ke Karamar Hukumar ta Madagali, inda suka yi wa wani dan banga a gona gunduwa-gunduwa, da kuma sace wasu mata 10.
Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, DSP Usman Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya yi karin bayani da cewa mutum 11 ne suka mutu, wasu da dama suka jikkata.
A yan kwanakin nan dai hare-haren ’yan kungiyar Boko Haram ya ta’azzara a yankin, inda ko a ranar Alhamis, an ruwaito ‘yan bindigar sun yi wa sojoji kwantan bauna, inda suka kashe sojoji uku, tare da kame wani mutum guda a garin Magar.
Rahotannin dai sun bayyana yadda lamarin ya faru da cewa ‘yan bindigar sun yi shiga irin ta ‘yan banga ne, don haka a tsammanin sojojin abokan aiki ne, wanda ya ba su damar kashe sojojin 3 da kame wani soja daya. Haka zalika an fafata tsakanin sojan Nijeriya da kuma ‘yan bindigar a garin Kichinga, duk dai a Karamar Hukumar ta Madagali a ranar ta Alhamis.
Sakamakon yawaitar wadannan hare- haren ‘yan bindigar, yanzu haka dai jama’a da dama daga yankin Karamar Hukumar ta Madagali suna gudun hijira zuwa Mubi, wasu kuma na komawa Yola.
Da yake yi wa LEADERSHIP Hausa karin bayani, dan Majalisa mai wakiltar Kananan Hukumomin Madagali/Michika a Majalisar wakilai ta tarayya, Hon. Adamu Kamale, ya bayyana cewa jama’ar yankin suna cikin mayuwacin hali tun bayan harin.

source leadership hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*