Yanda Ake Hada Yoghurt

YOGHURT (NONO)
• Nono
• Madara gwangwn 4
• Ruwa
A samu madara ta gari ki dora ruwa a wuta kamar cikin kwanansha idan yayi zafi sai ki dan kwaba madarar da ruwa kadan ki zuba dan karya kulle miki,sai ki kawo wani nonon kadan kamar ludayi biyu ki zuba,sai ki rufe ki kaishi guri me zafi ki aje,idan da safene zuwa yamma yayi zakiga yayi kauri,shikenan kin gama,insha Allahu anjima zamu kawo yadda zakiyi furarki da kanki.
KARIN BAYANI
yar uwa ba ayinsa da ruwan zartsi sai da na dadi.
daga Asma’u Garba

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*