Yanda Ake Hada Fura

FURA
____
• Gero
• Suga
• Kayan kamshi
• Ruwa
ki gyara geronki a surfa miki ki bushe ki wanke ki baza ya bushe ki sa citta da dan barkono kadan a nuko miki yayi laushi ki tankade da rariya me zaga zaga,
idan kin tankade sai ki juye garin a turmi ki dakashi sosai,san nan ki juyeshi ki dan yayyafa masa ruwa ki juyashi yadda zaki iya dun kuleshe,sai ki dinga curashi da dan girma har ki gama,
sai ki dora tukunya da ruwa idan ya tafasa sai ki kawo wannan garin da kika cura ki sassaka a ciki ki rufe ki barshi yayi ta dahuwa,idan yayi zakiga bayansa yayi ja ruwan kuma yayi kauri sai ki saukeshi ki dauko turminki ki saka a ciki ki fara dakawa idan kika daka gudan ya fashe sai ki zuba suga yadda kike so ki jujjuya shi sai ki debo wannan kiliftun bi ma ana ruwan dahuwar ki zuba amma karki cika ruwa sai kiyi ta dakawa ko nace kirbawa,zakiga tana hade jikinta to sai ki dandabeta da tabaryar san nan kiyi ta daka tsakiyar kiyi mata huda yadda 9zata fi fita sai ki kwakkwafeta ki yanyankata kamar awara,

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*