Wani Magidanci Ya Kashe mahaifiyarsa

Jami’an tsaro a garin Jos babban birnin jihar Filato suna ci gaba da binciken wani mutum dan shekaru 52 mai suna Brabo Kunde, bisa zargin kashe mahaifiyarsa mai kimanin shekaru 80 mai suna Mama Yakubu, ta hanyar sassara ta da adda.
Shi dai Brabo Kunde, wanda wata majiya ta tabbatarwa da wakilinmu cewa yana shaye-shayen kayan maye, ya kashe mahaifiyar tasa ne a safiyar ranar alhamis din da ta gabata a Unguwar Janta Mangoro da ke garin Jos.
Wani da ke makwabtaka da gidan marigayiyar mai suna Mista bictor Ali, ya bayyana wa Aminiya cewa, abin da ya faru shi ne, tun a daren ranar laraba mutane suka ga wanda ya aikata wannan mummunan aiki a buge, yana ta yin abubuwan da ba su dace ba. Da gari ya waye sai ya sanya mahaifiyar tasa ta dafa masa abinci ya ci, bayan da ya gama karyawa.’’Sai ya fito daga dakinsa ya kira mahaifiyar tasa, a lokacin da ya kira ta yana rike da adda a hanunsa, tana zuwa sai ya kama saranta daaddar, tana ta ihu tana neman taimako har sai da ta mutu. Da makwabta suka fito suka ga abin da ya faru, sai suka yi kansa, sai shi ma ya yi kansu da wannan addar, da kyar aka samu aka kwace addar.’’
Ya ce, ganin wannan mummunan aiki da Brabo Kunde ya yi, sai matasan Unguwar suka taru suka yi masa duka kamar ba zai tashi ba, wasu ma suka ce a sanya masa taya a kona shi. Sai wasu manyan unguwar suka hana. Mai unguwa ya je ya kirawo ’yan sanda suka kai shi asibitin kwararru na jihar Filato da ke garin Jos.
Wata majiya ta tabbatar wa wakilinmu cewa, Brabo Kunde yana zaune da mahaifiya tasa ne a gida daya tare da ’yayansa guda uku. Kuma ita mahaifiyar tasa ce take rike da wadannan yara.
Rundunar ’yan sandan jihar Filato ta tabbatar da cewa Brabo Kunde yana nan kwace a asibitin kwararru na jihar Filato da ke garin Jos kuma tana cigaba da bincike kan al’amarin.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*