Walcott Da Chamberlain Baza Su Buga Wasa Uku

Theo Walcott da Oxlade-Chamberlain ba za su buga wa Arsenal wasanni uku ba, sakamakon raunin da suka ji.
‘Yan wasan biyu sun ji rauni ne a lokacin da suke buga karawar da Sheffield ta fitar da Arsenal daga gasar Capital One Cup a ranar Talata.
Walcott ya gamu da taruwar jini ne a kafarsa, yayin da Chamberlain zai yi jinyar tsagewar tsoka shi ma a kafarsa.
Bayan da aka tashi daga karawar kociyan Arsenal Arsene Wenger, ya ce bai kamata ya yi amfani da manyan ‘yan wasansa ba.
‘Yan wasan biyu ba za su buga wa Arsenal fafatawar da za ta yi da Swansea City da Tottenham da kuma karawar da za ta yi da Bayern Munich a gasar cin kofin zakarun Turai ba.

Baza su buga wasan Arsenal da Swansea, Bayern Munich,  Tottenham 
naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*