Rasha ta amince ta hada hannu da Amurka domin yakar ISIL

Kasar Rasha ta bayyana aniyarta na aiki tare da ‘Yan tawayen Syria da kuma Amurka domin farwa mayakan ISIL da hare hare ta sama a Syria.
Ministan harakokin wajen Rasha Sergei Lavrov ne ya bayyana haka tare da yin kiran a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu a kasar ta Syria.
Wata majiya a Rasha kuma ta tabbatar da cewa shugaban kasar Syria Bashar al Assad ya amince ya shiga takarar zaben shugaban kasa a sabon zaben da Rasha ta bukaci a gudanar.
Sai dai ana hasashen yana da wahala bangaren adawa a Syria su amince da kudirin Bashar Al Assad na tsayawa takara a sabon zaben.
rfi hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*