Ouattara ya sake lashe zaben Ivory Coast

Shugaban kasar Ivory Coast, Alassane Ouattara, ya sake
lashe zaben shugaban kasar a karo na biyu.
Hukumar zaben kasar ta ce shugaba Ouattara ya yi
nasara a zaben da a ka gudanar ranar Lahadi da fiye da
kashi 83 cikin dari na kuri’un da aka kada.
Babban abokin hamayyarsa shi ne tsohon firayi ministan
kasar, Pascal Affi N’Guessan, wanda ya samu kashi tara
cikin dari na kuri’un, kuma ya yi takara ne a karkashin
jam’iyyar IPF ta tsohon shugaba Laurent Gbagbo wanda
Ouattara ya kayar da zaben shugaban kasar na shekarar
2010.
‘Yan takara na jam’iyyun hamayya da dama sun fice daga
yakin neman zaben inda suka yi korafin cewa ba za a
gudanar da zabe na gaskiya ba.
Sai dai masu sa ido kan zaben sun ce sun gamsu da
yadda zaben ya gudana.
Wannan dai shi ne babban zabe na farko tun bayan zabe
mai zafi sosai da aka gudanar a kasar a 2010, wanda ya
janyo barkewar yakin basasar da ya yi sanadiyar mutuwar
mutane 3000.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*