Oliseh ya gayyaci 'yan wasa 23 Super Eagles

Kociyan tawagar kwallon kafar Nigeria ta Super Eagles,
Sunday Oliseh ya gayyaci ‘yan wasa 23, domin fafatawa
da Swaziland a wasan neman gurbin a Gasar cin Kofin
Duniya ta 2018.
A cikin ‘yan wasan da aka gayyata har da Obafemi
Martins, wanda rabon da ya buga wa Super Eagles
tamaula shekaru biyu da suka wuce kenan.
Akwai kuma ‘yan wasa shida da suke murza leda a gida
da kuma suka samo wa Nigeria tikitin shiga Gasar cin
Kofin Nahiyar Afirka da za a yi a Rwanda a shekara mai
zuwa.
Karawar da Super Eagles za ta yi gida da waje, za ta fara
da ziyartar Lobamba a ranar 13 ga watan Nuwamba,
sannan ta karbi bakuncin wasa na biyu a ranar 17 ga
watan Nuwamba a Fatakwal.
Oliseh ya umarci dukkan ‘yan wasa da ya bai wa goron
gayyata da su isa otal din Bolton White Apartment da ke
Abuja, Nigeria, a ranar 8 ga watan Nuwamba domin fara
yin atisaye.
Ga jerin ‘yan wasan da Oliseh ya gayyata Super Eagles:
Masu tsaron raga: Carl Ikeme (Wolverhampton
Wanderers, Ingila); Ikechukwu Ezenwa (Sunshine Stars);
Dele Alampasu (Club de Sportivo Feirense, Portugal)
Masu tsaron baya: Abdullahi Shehu (Uniao da Madeira,
Portugal); Kalu Orji (Enugu Rangers); Elderson Echiejile
(AS Monaco); Chima Akas (Sharks); Leon Balogun (FSV
Mainz, Jamus); Godfrey Oboabona (Caykur Rizespor,
Turkiya); Efe Ambrose (Celtic, Scotland); Austin
Oboroakpo (Abia Warriors)
Masu wasan tsakiya: Ogenyi Onazi (SS Lazio, Italy); Paul
Onobi (Sunshine Stars); John Mikel Obi (Chelsea, Ingila);
Rabiu Ibrahim (AS Trencin, Slovakia); Wilfred Ndidi (KRC
Genk, Belgium); Sylvester Igbonu (UFA, Rasha)
Masu zura kwallo a raga: Ahmed Musa (CSKA Moscow,
Rasha); Moses Simon (KAA Gent, Belgium); Odion Ighalo
(Watford, England); Ezekiel Bassey (Enyimba); Alex Iwobi
(Arsenal, England); Obafemi Martins (Seattle Sounders,
Amurka)

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*