Najeriya ta tsallake zuwa gasar Afrika a Rwanda

Najeriya ta tsallake zuwa gasar Afrika ta matasa da ke
taka kwallo a gida da za a gudanar a Rwanda a badi,
bayan ta rike Burkina Faso babu ci a Ouagadougou.
Najeriya ta samu nasarar tsallakewa ne saboda nasarar
kwallaye biyu ta zira a ragar Burkina a karawa ta farko.
Kasashen da suka tsallake gasar sun hada da Rwanda
mai masaukin baki da Morocco da Tunisia da Mali da
Guinea da Nijar da Gabon da Jamhuriyyar Congo da
Uganda da Habasha da Zimbabwe da Zambia da kuma
Angola.
A 16 ga watan Janairun 2016 ne za a fara bude gasar a
kuma a 7 ga watan Fabrairu.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*