Nafisat Abdullahi ta maida martani ga Adam Zango dangane da sabon Aurensa

Nafisat Abdullahi ta maida martani  Adam A. Zango dangane da sabon Aurensa
Jarumar fina-finan Hausa ta Kanny wood, Nafisa Abdullahi ta nuna kishin ta karara dangane da sabon Auren da jarumi Adam A Zango ya yi a cikin makon nan.
Wani bincike da HAUSA TIMES tayi ta gano cewa abokan aikin jarumin na Kanny wood sun yi ta nuna farincikin su da fatan Alheri da taya Adam Zango murnar kara Aure amma banda jaruma Nafisat,
A madadin haka sai jarumar ta sanya wani hoto a shafin ta na Instagram wanda ke dauke da wani sako a turance dake cewa “Ba mamaki Allah ya hanani kai saboda dama miji nagari na roka sai kuma ba ka din bane”
Take-yanke magoya bayan jarumar suka shiga bata hakuri da fatan Alheri a karkashin hoton wanda ake ganin dama martani tayi wa Zango,
Idan dai ba’a manta ba a kwanakin baya jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram cewa tana matukar kaunar Adam A. Zango, tana mai fatan Allah ya zaba masu mafi alheri tsakanin ta da shi.
Nafisah ta ce, “Na san wannan mataki zai sa mutane su rika tambaya ta; ni kai na ban san amsar da zan ba su ba, ban iya boye-boye ba don haka ina son sa (Adam Zango ), kuma duk abin da ubangiji ya tsara a tsakaninmu, a shirye nake na dauka.”
Nafisah Abdullahi ta bukaci mutane da su yi mata fatan alheri a kan lamarin, ko su yi shiru, kamar yadda wani hadisi ya bayyana.
A ranar Litinin da ta gabata ne dai aka daura auren fitaccen jarumin Adam A Zango a asirce da amaryarsa Ummu Kulthum a  kasar Kamaru
Hausa Times

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*