Majalisa ta tantance karin ministoci biyar

Majalisar dattawan Najeriya ta tantance karin mutane
biyar da shugaban kasar ya mika mata domin nada su a
matsayin ministoci.
Wadanda majalisar ta tantance su ne Farfesa Adewale
Isaac Folorunso da Honourable Bawa Bwari Abubakar da
Geoffrey Onyeama, da Zainab Shamsuna Ahmed da
Birgadiya Janar Mansur Mohammed Dan’Ali da kuma
Pastor Usani Uguru Usani.
Shugaba Buhari dai ya aike wa Majalisar da da sunayen
mutane 37 domin a nada su ministoci, sai dai ya janye
sunan Alhaji Ahmed Musa Ibeto daga jihar Naija, bayan
da aka gano cewa sunayen mutane biyu aka mika daga
jihar.
A makon da ya gabata ne majalisar dattawan karkashin
jagorancin Sanata Abubakar Bukola Saraki ta tantance
tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi da wasu
mutanen.
Tuni majalisar ta amince da nadin mutane 18 daga cikin
mutanen 37 domin bai wa shugaba Buhari damar rantsar
da su a matsayin ministoci.
A ranar Laraba ake sa ran majalisar za ta ci gaba da aikin
tantance ministocin.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*