'Ba ma amfani da sojin haya'

Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta ce rundunar sojin kasar
ba ta amfani da sojojin haya, a yakin da ta ke yi da masu
tayar da kayar baya, a yankin arewa maso gabashin
kasar.
Kakakin hedikwatar tsaron ta Najeriya, Kanar Rabe
Abubakar ya shaida wa BBC cewa rundunonin sojin kasar
na da isassun dakaru masu kwarewar da za su iya yin
yakin ba tare da neman dauki daga wasu ba.
Ya kara da cewa sojojin da suke amfani da su su ne na
hadin gwiwa daga kasashen yankin tafkin Chadi da Benin
wadanda aka cimma yarjejeniya da su.
A baya dai an ba da rahoton cewa wasu sojojin haya
daga wasu kasashen waje na taimaka wa sojojin Najeriya
a yakin da suke yi da mayakan kungiyar Boko Haram.
Wasu ma na cewa nasarar da sojojin suka samu wajen
kwato garuruwan da Boko Haram ta kama ba ta rasa
nasaba da tallafi daga sojojin na haya.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*