Kotu ta umurci gwamnati Nijar ta biya iyalan Baare diyya

Iyalan tsohon shugaban kasar Nijar marigayi Ibrahim
Baare Mainassara, sun ce sun gamsu da hukuncin da
kotun ECOWAS ko kuma CEDEAO da ke zamanta a Abuja
ta yanke dangane da kisan tsohon shugaban mulkin
sojin.
Kotun dai ta yanke hukunci ne cewa an take hakkin
rayuwa ta tsohon shugaban kasar a matsayinsa na dan-
Adam, an kuma tauye ‘yancin iyalansa na zuwa kotu.
Don haka ne kotun ta umarci gwamnatin Nijar din da ta
biya diyya ta kimanin sefa miliyan dari hudu da talatin da
biyar, kwatankwacin dalar Amurka dubu 750 ga iyalan
marigayin.
A shekarar 2013 ne dai dangin marigayin su 11 suka kai
kara kotun ta ECOWAS suna neman ta tilasta wa
gwamnatin Nijar nemo wadanda suka kashe shi a
shekarar 1999, a kuma hukunta su.
Jibrin Baare, kani ne ga marigayi Ibrahim Baare
Mainasara ya yi wa Abdou Halilou karin bayani a kan
yadda suka ji da hukuncin.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*