Kotu ta dakatar da Sarki Sanusi II rushewa ko sauyawa wani gini a masarautar Kano fasali

Kotu ta dakatar da Sarki Sanusi II rushe ko sauyawa wani gini a masarautar Kano fasali
Wata babban Kotu ta dakatar da mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, daga rushewa ko sauyawa wani ginin masarautar Kano fasali har sai an kammala sauraren wata shara’a da aka shigar da shi,
Tun da farkon dai wani kawun Sarkin ne Alhaji Salim Bayero ya roki Kotun da ta dakatar da majalisar masarautar Kano, da Antoni Janar na jihar daga yunkurin da sukeyi na sauyawa masarauta fasali da kuma rushe wasu gine-gine dake fadar domin ginawa hakimai ofis,
Wuraren sune Ka’iya da Kachako da Gidan Rumfa da kuma makabarta
Alhaji Salim ya kuma roki Kotun da ta hana Sarkin na Kano daga tada mazauna Gidan Rumfa dake cikin masarautar bisa zargin cewa su bayin Saraki ne,
Da yake sauraren karar a ranar Juma’a Alkalin kotun mai shara’a, A.T Badamasi ya umurci Sarki Sanusi II da sauran wadanda ake kara kada su taba komi na masarautar su jira a kammala shara’ar,
Daga nan sai Alkalin ya tsaida ranar 12 ga watan Nuwamba domin soma sauraren ainihin karar da jikan Sarakin ya shigar,
Da yake karin haske ga manema labarai, Lauyan mai karar, Mista Sanusi Sadiq, yace sun kawo kara ne domin a hana Sarki Sanusi II rushe makabartar fada wacce a cikin ta ne aka binne sarakunan masarautar fiye da 13 da suka gabata,
Kuma a cewar sa rusa ta “zai batar da da-daddiyar al’adar masarautar mai dumbin tarihi”
Abubakar ya gayawa Kotun cewa tuni har Sarki ya soma baiwa wasu mazauna masarautar dake zaune a wuraren da aka kebe za’a rushe takardar su gaggauta tashi.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*