'Watakila Kompany ba zai buga wasa da United ba'

Watakila Vincent Kompany ba zai buga karawar da
Manchester City za ta yi da Manchester United a gasar
Premier a ranar Lahadi ba in ji Manuel Pellegrini.
Manchester United ce za ta karbi bakuncin Manchester
City a gasar cin kofin Premier a ranar Lahadi a Old
Trafford.
City ta saka Kompany daf a tashi a wasa a fafatawar da
ta doke Sevilla 2-1 a gasar cin kofin zakarun Turai da
suka yi a ranar Laraba.
Nicolas Otamendi da Eliaquim Mangala ne suka buga
wasa tare a ranar Laraban, kuma Pellegrini ya yaba da
rawar da suka taka.
Kompany ya yi jinyar raunin da ya ji a karawar da City ta
yi da Juventus a gasar zakarun Turai a ranar 15 ga watan
Satumba a Ettihad.
Kuma dan kwalllon mai tsaron baya, bai buga wa City
wasan Premier da ta yi da Bournemouth a ranar Asabar
ba.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*