Kazamar Gida Part 1

afar yana tsaye a tsakar gidansa bayan ya fito daga wanka ya kulle bandakin da mukulli wanda ya maidashi wajen shigarsa shi d’aya domin hatta matar gidan bai barinta ta shiga.
Gidan yake k’arewa kallo, rike yake da k’ugunsa. Alokacin bai wuce goma na safe ba amma har lokacin matar gidan bata da niyyar motsawa daga shimfida tun bayan daya matsa mata tayi sallar asuba ta koma gadon bata k’ara juyi ba ballantana takai ga tashi. Ya kai kallonsa ga tukunya wacce ke cike da sauran abinci tun na shekaranjiya,gasauran kayan wanke wanke nan da ta bada wankinsu ga almajiri har ruwa ya dakesu sunyi k’ura bata kwashesu ba. Cikin bakin ciki yakai dubansa inda ta tula uban shara har ya cika dustbin yana zuba,ga wani danko danko da k’asan gidan yayi wanda ke tabbatar da ba a wankeshi sai iyakar abunda ruwan sama ya wanke.
Ya girgiza kansa kawai ya ja kafarsa zuwa falon. Ko yunkurin cire takalminsa baiyi ba hakanan ya taka kafet din ya nufi dakinsa. Sai alokacin ya iya sauke numfashi mai dad’i,wani k’arni falon yakeyi wanda shiyasa sam bai kaunar matarsa tayi girki da kifi duk kuwa sanda tayi toh zaman falon ya gagareshi kenan. Daman ya take a kazanta ballantana ace tayi aikin kifi. Ranar babu zaman falon.
Gaba daya Jafar bashi da inda zai zauna yaji sanyi a gidansa daya wuce dakinsa. Duk da dakuna hud’u ne a gidan da katon falo guda daya sannan bandaki har uku ne amma kazancewarsu bazai bari ko kusa mutum mai tsafta yayi marmarin shigarsu ba. Dakinsa da kanshi yake gyarawa ya sanya turaren tsinke,wani lokacin idan yaga lokacin kasuwa zai kure sai ya gyara gadonsa ya kulle ya tafi da mukullin idan ya dawo yayi sharar tunda yasan koda yabar mukullin bazata gyara ba saima ta shige dakinsa ta kwanta ta k’ara hargitsa gadon a cewarta duk gidan babu inda tafison kwanciya sai dakin nasa.
Saida ya gama shirinsa tsaf ya sanya takalmansa sannan yayi duba ga matarsa dake sharar bacci babu abunda ya dameta. Cikin bakin ciki ya daki cinyarta da karfi,a firgice ta farka tana susa,kallon rain in wayo ta hau yi mishi. Shima harararta yakeyi
“Tashi ki koma dakinki zan fita na makara.”
Ta ja tsaki tana wani marairaice murya irin ta masu bacci
“Haba jafar(sunansa take kira kai tsaye),meye hakane? Ka dauki alhakina wallahi.”
Bai iya cewa komai ba,kayan daya cire ya shiga linkesu ya ajiye a saman akwatinsa. Ta mike tsaye tana gyara zaman zanin da tasha aikin girki dashi na dare har lokacin shine a jikinta.
“Ai na tuna,gwara daka tasheni. Ashe yau suna muke dashi a hotoro. Anti amina ai kasan ta haihu ko?”
Jafar dai gadonsa ya gyara tsaf ya jera filo. Jin da tayi baice komai bane ta kara matsowa tana goge miyan bacci
“Wai jafar bakaji bane?”
Sai lokacin ya dago ya dubeta,gaba daya tasha jinin jikinta ganin yanda ya hade rai tamkar wanda aka aikomasa da sakon mutuwa.
“SIYAMA!!!”
Ya kira sunanta a fusace. Ta turo baki don tasan sauran zancen,fadan nan dai data tsana zaiyi. Ba tare data amsa ba ta kauda kanta gefe.
“Siyama ke wace irin jinsi ce? Anya zan yarda ke din mutum ce kamar sauran mutane? Na soma tsorata ni Jafar kodai aljana na kawo gidana! Bakisan abunda ya dace ba siyama, na soma yarda kanki ba daya bane! Banda haka! Na tashi ko gaisuwar arziki ban samu awajenki ba! Ke baki iya ki tashi ki taimakamin da ko abin karin kumallo ba bayan kina sane cewa ba zama zanyi gidan ba zan fita neman kudi ne. Kin kwanta tamkar mai baccin mutuwa sai bacci kike shararawa! Yanzu kuma daga tashinki don son ki kara tabbatarwa da mutum ke cikakkiyar mara tunani ce shine har kike da bakin tambayata fita unguwa! Toh wallahi muddin kika sa kafarki kika fita daga gidan nan sai na sab’a maki Siyama! Saikin raina kanki wallahi. Sannan wallahi na dawo na sami gidan nan yana wannan tashin karnin sai kinsan namiji kike aure ba wanda ya rako maza ba. Ga shara can zan turo maki almajiri ki hadamishi ya zubar ya wanke dustbin da parker din. Fita ki bani waje zan rufe dakina.”
Siyama ta riga ta gama kaiwa bango,a fusace ta fita tana mai buga kofar da karfi. Har iska tana kad’o labulen dak e jikin windon d’akin. Jafar ya girgiza kansa bakin ciki goma da ashirin suka tarar masa. Ko shekara basu rufa ba da aure amma matsaloli sunfi adadin kwanakin dake cikin shekara guda yawa. Ya dauki wayoyi da mukullin mashin dinsa ya fito. Gam ya rufe dakinsa da mukulli ya jefa a aljihu ya fito. Tamkar zaiyi amai yakeji dakyar ya shiga dakin nata.
Tana zaune ta hade rai,wayarta a hannu da alama kira takeson yi. Ya bi dakin da kallo ya yamutse fuska,daki duk tarkacen kaya babu inda mutum zai zauna yaji sanyi. Bai damu da kallon da take watso mishi ba ya jefo mata dari biyar
“Gashi sai dare zan shigo kada kisa girkin rana dani.”
Da sauri ya fice domin ya gaji da jin warin dake busowa ta bandakinta wanda ke a wangale.
Ya ja mashin dinsa waje ya rufe mata kofa.
Ihun kukan bakin ciki siyama ta sanya,banda Allah Ya isa ba abunda take jerowa Jafar. A ganinta ai ya cuceta ace matar yayanta guda ta haihu,haihuwar ma na fari amma yace babu inda zataje.
Batayi wata wata ba ta lalubi lambar yayarta rumaisa ta danna mata kira.
Ringing biyu,ana uku ta amsa.
“Hello siyama ya dai? Kin fito?”
Siyama ta ciji lebbanta,hawayen bakin ciki suka k’aru
“Ina fa! Jafar ya cuceni anti rumaisa,yace babu inda zanje.”
Rumaisa ta runtuma ashariya
“Amma jafar dan kaza kaza ne! Banda ya rainawa mutane hankali yaushe akayi auren naku sannan duka duka fitarki nawa ne da har zaice kin fiye yawo bazakije ba? Yanaso ya soma raba zumunci tun ba’aje ko’ina ba? Wallahi bai isa ba,rabu dashi bari na yiwa Hajiya magana.”
Siyama ta tare ta da sauri
“A’a don Allah anti rumaisa ki rabu dashi kawai. Na amince bazan fita ba tunda yace zai dauki mataki muddin na yarda na fito bada izninsa ba.”
Rumaisa taja tsaki
“Banza uwar son miji,sai kiyita zama kin kare a haka jafar yana juyaki. Ki buga ki bawa aminar hakuri,amma tabbas ya dace ki tashi tsaye ki kwaci y’ancinki don wannan ba yi bane!”
Daga haka rumaisa ta yanke kiran. Siyama ta sharb’i kukanta har bataji sadda almajiri yayi ta kwada sallama ba. Saida ta nutsu sannan taji. A fusace ta fito idanuwanta cike taf da bala’i
“Wai lafiya ka ishi mutane da sallama? Menene?”
Yaron yace
“A’a maigidan ne yace nazo wai zan kwashe shara.”
Ta harareshi taja tsaki,shi dai yaro duk ya firgita kada ta kai mishi duka. Ta nuna inda dustbin din yake
“Ai gashican,kaje kayi ta kwasa.”
Daga haka tayi dakinta ta rufe kofar ta soma kiciniyar yin wanka saboda tsamin jikinta ya soma isarta. Idan bata mance ba rabonta da wanka tun safiyar jiya da Jafar ya matsa da bukatarsa,dolenta kuwa tayi wankan da babu niyya ba don haka ba yanda a kwana biyun nan takejin sanyin gari bazatayi ba. Ita kam tak’i jinin wanka da ruwan sanyi kamar yanda take jin kasalar d’ora ruwan zafi a risho.
Jafar kuwa tunda ya zauna a shago cikin kasuwa ya kasa maida hankali sosai kan sana arsa. Tunaninsa kacokam yana ga wannan muguwar halayya ta Siyama wanda yake neman hanyar kawo karshenta. Toh kodai ‘yar aiki zai nema mata ne? Saidai kuma ta yaya? Domin tun farko saida ya nemi hakan a wajenta ta hayayyako masa,wai ita sam bata son ‘yan aiki nan da nan sai su kwace maka miji su barka baki hangame. Karshe tace tafison almajiri ya barta duk da dai hakan bai kwanta masa ba sai don su zauna lafiya. Duk da d’abi’un Siyama,yana sonta matuk’a. Y’ar uwarsa ce kuma matarsa,ta yaya zai k’i d’iyar kanin mahaifinsa? Bayason kai k’ararta kada ayi mishi kallon marar hakuri ace ko shekara bata rufa ba ya soma k’orafi.
“Jafar wai yau lafiya kake?”
Ya dago kansa ya dubi abokin aikinsa,Ibrahim. Murmushin yak’e yayi
“Lafiya,kaina ke d’an ciwo.”
“Allah Ya sauwake toh.”
Ya amsa da amin. Ya tuno a matsalarsa har da yunwa,dole ya mik’e ya shiga cikin kasuwa don ziyartar Ladi mai abinci. Yana son cin abincinta,gata dai k’aramar yarinyar da bata fi shekaru goma sha shida ba amma akwai tsafta hakanan abincinta zakaci shi lafiya lau. Sam,bata da hayaniya irin ta sauran masu siyar da abinci.
Tare sukeyin aikin dahuwar da mamanta,saidai kwana biyu Maman babu lafiyar jiki,ladi keyi.
Har nauyi yakeji ace da m atarsa amma yana cin abinci a waje duk saboda rashin tsaftar muhalli da rashin gyara tukunya. Ladi har ta sanshi sosai saboda babu ranar da baya zuwa shagonsu cin abinci.
Tunda ya shiga shagon ta hangoshi. Ta sakar masa murmushi adaidai lokacin da take ajiye kwano taf da abinci agaban teburin wasu. Ya maida mata martanin murmushin kafin ya maida hankali kan wayarsa.
“Assalamu alaika. Barka da zuwa yayana. An iso lafiya? Ya antina?”
Wani sanyi ya kwanta luf a zuciyarsa,abunda ya gaza samu kenan a gidansa. A rayuwar Jafar yanason a bashi girma muddin ya zamana ya girmewa mutum koda da mintoci ne. Shiyasa Ladi take burgeshi,murmushi ya k’ara sakar mata alokacin da yake amsa sallamarta.
“Wa alaikissalam ‘yar nijar. Lafiya lau nake,ya jikin mama?”
Ladi wacce har lokacin murmushi bai kaura daga kan fuskarta ba ta bashi amsa
“Mama ai ta samu sauki sosai,mungode Allah. Watakila ma gobe ka ganta tazo. Ai tana yawan tambayarka kasan bata mance manyan customers d’inta.”
Yayi ‘yar dariyar yak’e saboda kunyar da yaji,kenan dai har an sanyashi layin manyan customers? Hum! Siyama ta cuceshi. Ladi ta katse mishi tunani
“Bari na hado maka abincin.”
Tayi gaba ba tare data jira abunda zai umarci a kawomasa ba. Toh menene bata sani ba tunda ba yau ne ya soma zuwa shagonsu ba?
Minti biyu sai gatanan da saurinta,hannunta dauke da kwanukan abinci ta ajiye agaban teburinsa. Lafiyayyen tuwo ne da miyar danyar kub’ewa yaji nama da ganda sai daddad’an kamshi ke tashi. Kallo d’aya ya yiwa abincin babu wata wata ya soma ci bayan ya wanke hannu da ruwan data ajiye.
Yana ci yana tunanin inama ace haka Siyamarsa ta iya dahuwa,inama tana da tsafta koda rabin ta Ladi ce.
Yunwar daya kwaso ne ya mantar dashi inda yake, hakan yasa bai dago ya kalli kowa ba har saida ya kammala cin abinsa. Rabonsa da abinci tun jiya da rana dayazo shagon Ladi ya narki shinkafa da miya mai d’an karen dadi. Koda ya koma gidan da dare,bai iya cin abincin Siyama ba saboda k’arnin kifi dake tashi.
Ladi kuwa tana wanke kwanuka saidai rabin hankalinta yana ga Jafar. Tana tausaya masa sosai. Bata mantawa a baya kafin Jafar yayi aure,ya kasance mutum ne mai yawan wasa da dariya. Sukanzo harda abokan kasuwancinsa su ci abinci a shagon har ma su jima suna hirarsu kafin su tattara su koma cikin kasuwa. Saidai fa ba sa ido ba,ta fahimci Jafar na baya dana yanzu sun bambanta matuk’ar gaske. Wannan Jafar din ya rame,bashi da wasan nan,dariyarsa bata tsawo. Idan yazo daga gaisuwa ba abunda ke shiga tsakaninsu. A zaton Ladi,aure ai yakan chanja rayuwar mutum daga bakin ciki zuwa farin ciki saidai auren Jafar ba haka yake ba.
Bata da hujjar cewa ba auren soyayya yayi da anti siyama ba,don ita shaida ce akan yanda yake zuzuta siyama a gabansu. Har suyita dariya ita da mama. Hatta hotunan siyama ya tab’a nuna mata don har gajiya tayi ta mik’a masa wayar ganin sunk’i k’arewa.
Duk da bata shiga hurumin da bai shafeta ba,saidai yau kam taci d’amarar tambayar Jafar matsalarsa. Haka kawai tana jinsa tamkar wani yayanta musamman daya kasance bata da wani d’an uwa babba ko k’arami. Ita kadai ce wajen mamanta. Don haka ta kife kwanukan a kwando,ta gyara zaman hijabinta ta nufi inda Jafar ke zaune yana kora ruwan lemo a cikinsa…
Xaki debo ruwan dafa kanki…

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*