Jam'iyyar APC Ta Gode Ma Buhari, Majalisa

Jam’iyyar APC ta jihar Rivers ta bayyana cewa tabbatar da Rotimi Amaechi da aka yi a matsayin minista nasara da aka samu akan shaidanun. “Shaidanun nan wadanda suke samun taimako saga Gwamna Nyesom Wike, sunyi matukar kokari domin hana Amaechi zama minista. Amma Ubangiji ta hanyar Buhari da majalisar dattawa ya wargaza al’amarin su.
“Wannan ranar 19 ha watan Oktoba ranar tarihi cewa jihar Rivers domin kuwa duk da kokarin shaidanin nan Wike, Amaechi ya zama ministan Najeriya duk da korafi korafen da aka kai a kanshi.”
Shugaban Jam’iyyar APC ta Rivers, Dacta Davies Ibiamo Ikanya ne ya fidda takardar wadda ya tattauna ma hannun a ranar Alhamis 29 ga watan Oktoba a Fatakwal.
Jam’iyyar APC kuma ya yaba ma Shugaba Muhammadu Buhari daya zabi Amaechi da sauran ministocin. Sun bayyana cewa Wike bai yi jihar Rivers wani abun arziki ba. Sannan ya hanyoyi ma jihar komawa baya.
Jam’iyyar, ta shawarci Musulmai suyi amfani da ranar Juma’a 30, ga watan Oktoba da kuma Kirista ranar Lahadi 1, ga watan Nuwamba domin Ubangiji Allah ya kubutar da al’umma daga masu baba kere.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*