Hatsarin mota ya kashe mutane 40 a Faransa

Mutane sama da 40 ne suka mutu a lokacin da motar bas
din da suke ciki ta yi karo da wata motar daukar kaya a
kudu maso yammacin Faransa.
Motocin biyu sun yi karo ne a gabashin birnin Bordeaux,
mintuna kadan bayan sun hau kan hanya.
Motar bas din na dauke ne da ‘yan fansho da ke kan
hanyar su ta zuwa yawon bude idanu.
Karon da motocin biyu suka yi ya sa suka kama da wuta.
A kalla mutane 41 da ke cikin bas din da kuma direban
babbar motar ne suka mutu sakamakon wutar da ta kona
su.
Mutane takwas ne suka tsira, biyar daga cikinsu kuma
sun samu raunuka.
Shugaban Faransa, Francois Hollande, ya bayyana a
shafinsa na Twitter cewa gwamnatinsa “ta dauki matakin
gaggawa a kan hatsarin”.
Wannan shi ne hatsarin mota mafi muni da aka yi a kasar
tun bayan wanda aka yi a shekarar 1982 wanda ya yi
sanadiyar mutuwar a kalla mutane 52.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*