Faransa za ta jagoranci taron tattauna rikicin Syria

Faransa ta bayyana cewa a gobe Talata ne za ta
jagoranci taron tattauna rikicin Syria tare da dukkanin
bangarorin da ke rikici a kasar.Kasashen da aka
gayyata a taron da za’a gudanar a birnin Paris sun
hada da Saudiya da Turkiya
kasar Iran da Rasha ba sa cikin kasashen da Faransa ta
gayyata a wannan taron kasancewar su masu banbanci
ra’ayi a rikicin na Syria.
Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta ce a gobe Talata ne
Laurent Fabius zai jagoranci taron tattauna rikicin Syria
wanda zai kunshi wasu masu ruwa da tsaki a rikicin
kasar.
Za’a gudanar da taron ne dai a birnin Paris kuma Faransa
ta gayyaci Jamus da Birtaniya da Saudiya da Amurka
aminanta domin tattauna yadda za’a shawo kan rikicin
kasar ta Syria.
Wannan kuma na zuwa ne a yayin da ya rage rana guda
shugabannin kasashen Rasha da Amurka da Turkiya da
Saudiyya su gudanar da taro a Vienna ba tare da Faransa
ba.
Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius yace
za’a yi taron ne ba tare da babban jami’in diflomasiyar
Rasha ba Sergie Lavrov.
An dadde dai manyan kasashen duniya na tattauna kan
rikicin Syria amma ba tare da fito da hanyoyin
magance rikicin kasar ba da ya lakume rayukan
dubban mutane tare da sa miliyoya gujewa gidajensu.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*