Buhari Zaya Halarci Wani Taro A Indiya

A gobe Talata 27 ga watan Oktoba, Shugaba Muhammadu Buhari zaya bar Abuja zuwa New Delhi, babban birnin kasar Indiya inda zaya halarci taro na 3 na Indiya da Afirika.

A wata takarda da Femi Adesina, mai taimaka ma Shugaban Kasa Akan hudda da Jama’a ya fitar, Adesi a ya bayyana cewa taron zaya habbaka tattalin arzikin Afirika da Indiya.
Mai hudda da Jama’an ya bayyana cewa, shugabannin duniya zasu halarci taron wanda hakan zaya habbaka tattalin arzikin Afirika Dana Indiya.
Ya kuma bayyana cewa Shugaba Buhari zaya gana da Firaym Minista Modi da mu karraba gwamnatin Indiya. Kafin dawowar shi Najeriya a ranar 30 ga watan Oktoba, Shugaba Buhari zaya gana da shuwagabannin kamfanoni dana kasar Indiya.
A cikin tawagar Buhari akwai gwamnonin Kano da Delta. Sannan kuma mai bashi shawara akan sha’anin tsaro, Babagana Munguno.
Sannan akwai sakatarorin ma’aikatun Wuta, Sadarwa, Fasaha, Cinikayya da kuma harkokin kasashen waje.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*