Biritaniya na horar da sojojin Nigeria

Biritaniya na horar da sojojin Najeriya 150 dabarun yaki
da ta’addanci.
Ana gudanar da wannan horo a makarantar horar da
hafsoshin soji ta Najeriya da ke Jaji a jahar Kaduna.
Sojojin Biritaniya za su rika koya wa sojojin Nigeria masu
mukaman Warrant Officers da na kasa da su dabarun kai
farmaki da kai dauki, da sauran dabaru na yaki da tayar-
da-kayar-baya.
Wannan dai wani shiri ne na hadin gwiwa tsakanin
Biritaniya da Nigeria.
Manjo Janar Sanusi Mu’azu ya bayyana wa BBC cewa
babu shakka horon zai inganta ayyukansu.
A yanzu haka dai Nigeria na yaki da kungiyar Boko
Haram, yakin da ta lashi takobin kammala shi zuwa
watan Disamba.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*