Ba zan sauya yadda nake wasa ba — Costa

Dan wasan Chelsea Diego Costa ya ce shi ba waliyyi ba
ne don haka ba zai sauya yadda yake taka leda ba.
Sau biyu ana haramtawa dan wasan buga wasanni uku
bayan ya taka dan wasan Liverpool Emre Can da kuma
taho-mu-gamar da suka yi da dan wasan Arsenal, Laurent
Koscielny.
Costa ya shaida wa Football Focus cewa,”Na kawo inda
nake ne saboda salon da nake amfani da shi wajen take
leda. Ba zan canza salon ba saboda kawai mutane suna
maganganu.”
Ya kara da cewa, “Ina tsammani kwallon kafa na da
fuskar nishadantarwa da kuma fuskar yi wa mutane baro-
baro. Kuma ‘yan wasa suna nuna fuskonin biyu ne, don
haka ya kamata mutane su saba da hakan.”

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*