'Buhari ba zai iya yakar cin hanci ba'

Wani fitaccen dan siyasa kuma tsohon Jakadan Nijeriya
a kasar Switzerland, Ambasada Yahaya Kwande, ya ce
duk da cewa shugaba Muhammadu Buhari yana da
kyakkyawar niyya wajen kawo karshen matsalar rashawa
da cin hancin a kasar amma ba zai iya magance wannan
matsala ba.
Sai dai kuma ya ce yana sane da irin kokarin da Buharin
yake yi da kuma irin tsoron sa da mutane suke yi
wadanda ya ce sun taimaka gaya wajen rage matsalar.
Ambassada Kwande ya kara da cewa matsalar rashawa
da cin hanci a Najeriya ta yi katutun wadda kawar da ita
farad daya zai yi wuya, a inda yake ganin shugaba Buhari
zai iya dasa dan-ba ne kawai wanda daga bisani za a
mori ribar hakan a nan gaba.
Dangane kuma da zarge-zargen da ‘yan jam’iyyar adawa
ta PDP suke yi kan cewa yaki da cin hanci da rashawar
da gwamnatin Buharin take yi wani abu ne mai kama da
bita da kulli, ambassada Kwanden ya ce shure-shure ne
kawai wanda aka ce ba ya hana kaza mutuwa.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*