Aston Villa ta sallami Tim Sherwood

Aston Villa ta raba gari da kociyanta Tim Sherwood, bayan da ya jagoranci kungiyar watanni takwas.
Villa ta kori Sherwood daga aiki bayan da Swansea ta doke ta 2-1 a gasar Premier da suka yi a ranar Asabar a Villa Park.
Kuma doke ta da aka yi shi ne rashin nasara a wasanni shida da aka ci Villa a jere da hakan ya sa take mataki na 19 a kan teburin Premier.
Villa ta nada kociyan karamar kungiyar mai horas da matasa ‘yan kasa da shekaru 21 Kevin McDonald a matsayin rikon kwarya.
Sherwood wanda ya je Villa a watan Fabrairu ya kai kungiyar wasan karshe a kofin FA, sai dai kuma wasa daya ya ci daga guda 10 da ya yi a gasar Premier bana.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*