Ana gudanar da zaben shugaban kasa a Tanzania

A Tanzania da ke yankin gabashin Afirka ana gudanar da zaben shugaban kasar a wannan lahadi, zaben da ake ganin cewa shi ne mafi zafi a tsakanin ‘yan takara tun bayan samun ‘yancin kan kasar.
Shugaban kasar Jakaya Kikwete dai ba ya daga cikin ‘yan takara, to sai dai yana goya wa dan takarar jam’iyyarsa CCM ministan ayyuka John Magufuli, to sai dai tsohon firaministan kasar Edward Lowassa, ya fice daga jam’iyar tare da kulla kawance da ‘yan adawa.
Sama da mutane milyan 23 ne ke jefa kuri’a a wannan zabe na shugaban kasa da na kananan hukumomi da kuma ‘yan majalisun larduna.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*