Connect with us

Labarin Wasanni

An tuhumi Mourinho da halin rashin da'a

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tuhumi Jose Mourinho
da nuna rashin da’a kan munanan kalamai da halayya da
ya nuna a karawar da West Ham ta ci Chelsea 2-1.
A ranar Asabar ce West Ham ta doke Chelsea da ci 2-1 a
gasar Premier wasan mako na 10 da suka yi a filin wasa
na Boleyn Ground.
Haka kuma an sallami Mourinho da mataimakinsa Silvino
Louro da kuma dan wasansa Nemanja Matic daga cikin
wasan a karawar.
Hukumar ta kuma tuhumi kungiyoyin biyu da kasa
tsawatarwa da ‘yan wasansu, ta kuma ba su daga nan
zuwa 29 ga watan Oktoba domin su kare kansu.
Chelsea na fuskantar biyan tara ta kudi £25,000 saboda
‘yan wasanta biyar da aka bai wa katin gargadi a karawa
biyar da aka doke ta.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook

Advertisement

Trending