An kai harin bam a Yola

Ganau a birnin Yola da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya sun ce an tayar da bam a wani Masallaci da ke Jimeta.
Lamarin ya faru ne a Masallacin Jambutu da ke Jimeta a daidai lokacin da ake tayar da Sallar Juma’a.
Rahotanni na nuna cewa masu aikin ceto na can yanzu haka suna kwasar gawawwaki da kuma wadanda suka jikkata.
Ba a dai sani ba ya zuwa yanzu ko dasa bam din aka yi a masallacin ko kuma harin kunar bakin wake ne.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*