An cafke ‘Yan Boko Haram 45 a Lagos

Jami’an tsaro a Najeriya sun kama wasu mutane 45 da
ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne wadanda ke
kulle-kullen kai jerin hare hare a gidajen da ke Dolphin
Estate a Ikoyi, Jihar Lagos.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito majiyar
jami’an ‘yan sandan farin kaya na cewar an kama akalla
mutane 60 a sassa daban-dabam na birnin Lagos,
sakamakon bayanan sirin da aka tattara, kuma tuni aka
gabatar da su a gaban kotu a ranar Juma’a, inda aka
bukaci ci gaba da tsare su a gidan yari har sai an
kammala bincike.
Bayanai sun ce an saki 15 daga cikin su kuma yanzu
haka ana tsare da 45.
Gidajen Dolphin dai sun kunshi na manyan mutane
yawancinsu ma’aikatan mai a unguwar Ikoyi.
Mahukuntan Lagos sun nemi taimakon al’umma su
taimaka da bayanai akan duk wani yunkuri na kai hari a
Jihar.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*